1 Isra'ila kurangar inabi ce mai bansha'awaWadda yake ba da 'ya'ya da yawa.Ƙara yawan arzikinsu,Ƙara gina bagadansu.Ƙara yawan wadatar ƙasarsu.Ƙara kyautata ginshiƙansu.
2 Zuciyarsu ta munafunci ce,Yanzu tilas za su ɗauki hakkin laifinsu,Ubangiji zai farfashe bagadansu da ginshiƙansu.
3 Gama yanzu za su ce,“Ba mu da sarki,Domin ba mu ji tsoron Ubangiji ba.Amma me sarki zai yi mana?”
4 Surutai kawai suke yi,Suna yin alkawaran ƙarya,Don haka hukunci zai zaburo kamar muguwar ciyawa mai dafi a kunyoyin gona.
5 Mazaunan Samariya suna rawar jikiDomin ɗan maraƙin Bet-awen,Mutane za su yi makoki dominsa,Firistoci matsafa, za su yi kururuwa dominsa,Da kuma darajarsa wadda ta rabu da shi.
6 Za a kai ɗan maraƙin a AssuriyaDon a biya wa sarki haraji.Za a kunyatar da Ifraimu,Isra'ila kuwa za ta ji kunya saboda shawararta.
7 Sarakunan Samariya za su ɓace,Kamar kumfa a bisa ruwa.