4 Surutai kawai suke yi,Suna yin alkawaran ƙarya,Don haka hukunci zai zaburo kamar muguwar ciyawa mai dafi a kunyoyin gona.
5 Mazaunan Samariya suna rawar jikiDomin ɗan maraƙin Bet-awen,Mutane za su yi makoki dominsa,Firistoci matsafa, za su yi kururuwa dominsa,Da kuma darajarsa wadda ta rabu da shi.
6 Za a kai ɗan maraƙin a AssuriyaDon a biya wa sarki haraji.Za a kunyatar da Ifraimu,Isra'ila kuwa za ta ji kunya saboda shawararta.
7 Sarakunan Samariya za su ɓace,Kamar kumfa a bisa ruwa.
8 Za a hallaka masujadan tuddai na Awen inda Isra'ila suke yin zunubi,Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su yi girma a bagadansu.Za su ce wa manyan duwatsu, “Ku rufe mu!”Su ce wa tuddai, “Ku faɗo bisa kanmu!”
9 Ubangiji ya ce, “Tun daga kwanakin Gibeya, kun yi zunubi, ya Isra'ila!Tun daga wancan lokaci kuka yi ta ci gaba.Ashe, yaƙi ba zai tarshe su a Gibeya ba?
10 Zan fāɗa wa waɗannan mutane masu zunubi, in hukunta su.Za a tattara al'ummai, su yi gāba da su,Za a hukunta su saboda yawan zunubansu.