1 “Ka ce wa 'yan'uwanka maza, ‘Ku mutanena ne,’ ka kuma ce wa 'yar'uwarka, ‘Kin sami jinƙai!’
2 Ku roƙi uwarku,Gama ita ba matata ba ce,Ni kuma ba mijinta ba ne.Ku roƙe ta ta daina karuwancinta,Ta rabu da masu rungumar mamanta.
3 In ba haka ba, sai in yi mata tsiraici,In bar ta kamar ran da aka haife ta.In maishe ta kamar jeji,In bar ta kamar busasshiyar ƙasa,In kashe ta da ƙishi.
4 Ba zan yi wa 'ya'yanta jinƙai ba,Domin su 'ya'yan karuwanci ne