2 Sai na ba da sadakinta a bakin tsabar azurfa goma sha biyar, da buhu biyu na sha'ir.
3 Sa'an nan na ce mata, “Ki keɓe kanki kwanaki da yawa domina, kada ki yi kwartanci, ki kwana da wani, ni kuma ba zan shiga wurinki ba.”
4 Gama mutanen Isra'ila za su zauna kwanaki da yawa ba sarki, ba shugaba, ba sadaka, ba al'amudi, ba falmaran, ba kan gida.
5 Bayan wannan mutanen Isra'ila za su komo su nemi Ubangiji Allahnsu, da Dawuda, sarkinsu. Da tsoro za su komo zuwa wurin Ubangiji domin alheransa a kwanaki na ƙarshe.