5 Me za ku yi a ƙayyadaddiyar ranar idi?Da a ranar idin Ubangiji?
6 Ga shi kuma, suna tafiya zuwa halaka,Masar za ta tattara su,Memfis za ta binne su.Ƙayayuwa za su mallaki abubuwan tamaninsu na azurfa.Sarƙaƙƙiya za ta tsiro a cikin alfarwansu.
7 Ranar hukunci ta zo, ranar ramako ta iso,Isra'ila za ta sani!An ce annabi wawa ne,Mutumin da yake da ruhu kuwa mahaukaci ne,Saboda yawan muguntarku da ƙiyayyarku.
8 Ifraimu mai tsaro ne a gaban Allahna, annabi kuwa,Duk da haka sun zama kamar mai kafa tarkon kama tsuntsu, a farkon kaka.Akwai ƙiyayya a cikin Haikalin Allahnsu.
9 Sun yi zurfi cikin rashin gaskiyaKamar a kwanakin Gibeya,Ubangiji zai tuna da muguntarsu.Zai hukunta su saboda zunubansu.
10 Ubangiji ya ce, “Na iske Isra'ila a jeji kamar inabi,Na ga kakanninku kamar nunan fari na 'ya'yan ɓaure,Amma da suka zo Ba'al-feyor, sai suka keɓe kansu ga Ba'al.Suka zama abin ƙyama kamar abin da suke ƙauna.
11 Darajar Ifraimu za ta tashi kamar tsuntsu,Ba haihuwa, ba juna biyu, ba ɗaukar ciki!