29 Kowa ya ci, ya kuma sha, ba tare da faɗaka da jikin Ubangiji ba, ya jawo wa kansa hukunci ke nan, ta wurin ci da sha da ya yi.
30 Shi ya sa da yawa daga cikinku suke da rashin lafiya da rashin ƙarfi, har ma waɗansu da dama suka yi barci.
31 Amma in da za mu auna kanmu sosai, da ba za a hukunta mu ba.
32 In kuwa Ubangiji ne yake hukunta mu, to, muna horuwa ke nan, don kada a yanke mana hukunci tare da sauran duniya.
33 Saboda haka, ya 'yan'uwana, in kuka taru don cin abinci, sai ku jiraci juna.
34 In kuwa wani yana jin yunwa, sai yă ci a gida, kada yă zamana taronku ya jawo muku hukunci. Batun sauran abubuwa kuwa, zan ba da umarni a kai sa'ad da na zo.