5 Domin kuwa kamar yadda muke shan wuya ƙwarai, irin wadda Almasihu ya sha, haka kuma ake yi mana ta'aziyya ƙwarai, ta wurin Almasihu.
6 Ko ana wahalshe mu ma, ai, saboda ta'azantuwarku ce, da kuma lafiyarku. Ko ana ta'azantar da mu, ai, saboda ta'azantuwarku ce, wadda take sa ku, ku jure wa irin wuyan nan, da muke sha.
7 Sa zuciyarmu a kanku ƙaƙƙarfa ce, domin mun sani, kamar yadda kuka yi tarayya da mu a cikin shan wuya, haka kuma, za ku yi tarayya a cikin ta'aziyyar.
8 'Yan'uwa, ba ma so ku jahilta da wahalar da muka sha a ƙasar Asiya, domin kuwa mun ji jiki ƙwarai da gaske, har abin ya fi ƙarfinmu, har ma muka fid da tsammanin rayuwa.
9 Har ma muka ji kamar hukuncin kisa aka yi mana, wannan kuwa don kada mu dogara ga kanmu ne, sai dai ga Allah, mai ta da matattu.
10 Shi ne ya kuɓutar da mu daga muguwar mutuwa a fili, zai kuwa kuɓutar da mu, ga shi kuma muke dogara yă kuɓutar da mu har ila yau.
11 Ku ma sai ku taimake mu da addu'a, domin mutane da yawa su gode wa Allah, ta dalilinmu, saboda albarkar da aka yi mana, ta amsa addu'o'i masu yawa.