13 Irin waɗannan mutane manzannin ƙarya ne, mayaudaran ma'aikata, suna mai da kansu kamar su manzannin Almasihu ne.
14 Ba abin mamaki ba ne kuwa, domin ko Shaiɗan ma da kansa, yakan mai da kansa kamar shi mala'ikan haske ne.
15 Don haka, ba abin mamaki ba ne in bayinsa ma sun mai da kansu kamar su bayi ne na aikin adalci. A ƙarshe za a saka musu gwargwadon ayyukansu.
16 Ina sāke faɗa, kada wani ya zaci ni wawa ne. In kuwa kun zaci haka nake, to, ku ji ni wawa ne, don ni ma in samu in taɓa 'yar taƙama kaɗan.
17 Abin nan da nake faɗa fa, ba bisa ga umarnin Ubangiji nake faɗa ba, sai dai magana ce irin ta wawa, wadda yake yi gabagaɗi, yana fariya,
18 da yake mutane da yawa suna fariya irin ta 'yan adam kawai, ni ma zan yi.
19 Ai, ku kam, hikimarku har ta kai ga jure wa wawaye da murna!