15 Duk wannan fa don amfaninku ne, domin alherin Allah ya yaɗu ga mutane masu yawa, ta haka ya zama sanadin yawaita godiya ga Allah, domin a ɗaukaka Allah.
16 Saboda haka ba mu karai ba, ko da yake jikinmu na mutuntaka yana ta lalacewa, duk da haka, ruhunmu a kowace rana sabunta shi ake yi.
17 Don wannan 'yar wahalar tamu, mai saurin wucewa ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci.
18 Domin ba abubuwan da ido yake gani muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa, gama abubuwan da ake gani, masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne.