18 Duk wannan kuwa yin Allah ne, shi da ya sulhunta mu da kansa ta wurin Almasihu, ya kuma ba mu aikin shelar sulhuntawar,
19 wato, Allah ne, ta wurin Almasihu, yake sulhunta 'yan adam da shi kansa, ba ya kuwa lasafta laifofinsu a kansu ba, ya kuma danƙa mana maganar nan ta sulhuntawa.
20 Saboda haka, mu jakadu ne na Almasihu, wato, Allah na neman mutane ta wurinmu. Muna roƙonku a madadin Almasihu, ku sulhuntu da Allah.
21 Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi zunubi saboda mu, domin mu mu sami adalcin Allah ta wurinsa.