5 Saboda haka, na dai ga lalle ne in roƙi 'yan'uwan nan su riga ni zuwa a gare ku, su tanada baiwar nan da kuka yi alkawari kafin in zo, domin a same ta a shirye, ba tare da matsawa ba, sai dai kyautar sa kai.
6 Abin la'akari fa, shi ne wanda ya yi ƙwauron yafa iri, gonarsa za ta yi masa ƙwauron amfani, wanda kuwa ya yafa a yalwace, sai ya girba a yalwace.
7 Sai kowa yă bayar yadda ya yi niyya, ba tare da ɓacin rai ko tilastawa ba, domin Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai.
8 Allah kuwa yana da iko yă ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki.
9 Kamar yadda yake a rubuce cewa,“Ya ba gajiyayyu hannu sake,Ayyukansa na alheri madawwama ne.”
10 Shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, ya riɓanya shi, ya kuma yawaita albarkar ayyukanku na alheri.
11 Za a wadata ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa a yalwace, bayarwar nan kuwa da za ku yi, za ta zama sanadin godiya ga Allah ta wurinmu.