10 A ƙarshe kuma, ku ƙarfafa ga Ubangiji, ga ƙarfin ikonsa.
11 Ku yi ɗamara da dukan makamai na Allah, don ku iya dagewa gāba da kissoshin Iblis.
12 Ai, famarmu ba da 'yan adam muke yi ba, amma da mugayen ruhohi ne na sararin sama, masarauta, masu iko, da waɗanda ragamar mulkin zamanin nan mai duhu take hannunsu.
13 Saboda haka, sai ku ɗauki dukan makamai na Allah, domin ku iya dagewa a muguwar ranar nan, bayan kuma kun gama kome duka, ku dage.
14 Saboda haka fa ku dage, gaskiya ta zama ɗamararku, adalci ya zama sulkenku,
15 shirin kai bisharar salama ya zama kamar takalmi a ƙafafunku.
16 Banda waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kiban wutar Mugun nan da ita.