18 Sai ga waɗansu mutane ɗauke da wani shanyayye a kan shimfiɗa, suna ƙoƙari su shigar da shi su ajiye shi a gaban Yesu.
19 Da suka kasa samun hanyar shigar da shi saboda taro, suka hau a kan soron, suka zura shi ta tsakanin rufin soron duk da shimfiɗarsa, suka ajiye shi a tsakiyar jama'a a gaban Yesu.
20 Da Yesu ya ga bangaskiyarsu sai ya ce, “Malam, an gafarta maka zunubanka.”
21 Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka fara wuswasi cewa, “Wane ne wannan da yake maganar saɓo? Wa yake iya gafarta zunubi banda Allah shi kaɗai?”
22 Da Yesu ya gane wuswasinsu, ya amsa musu ya ce, “Don me kuke wuswasi haka a zuciyarku?
23 Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi, ka yi tafiya’?
24 Amma domin ku sakankance Ɗan Mutum na da ikon gafarta zunubi a duniya”, sai ya ce wa shanyayyen, “Na ce maka, tashi, ka ɗauki shimfiɗarka, ka tafi gida.”