24 Ya kawo musu wani misali kuma, ya ce, “Za a kwatanta Mulkin Sama da mutumin da ya yafa iri mai kyau a gonarsa.
25 Sa'ad da mutane suke barci, sai anokin gābansa ya je ya yafa irin wata ciyawa a cikin alkamar, ya tafi abinsa.
26 Da shukar ta tashi, ta yi ƙwaya, sai ciyawar ta bayyana.
27 Sai bayin maigidan suka zo, suka ce masa, ‘Maigida, ashe, ba kyakkyawan iri ka yafa a gonarka ba? To, ta yaya ke nan ta yi ciyawa?’
28 Sai ya ce musu, ‘Wani magabci ne ya yi wannan aiki.’ Bayin suka ce masa, ‘To, kana so mu je mu cire mu tara ta?’
29 Amma ya ce, ‘A'a, kada garin cire ciyawar ku tumɓuke har da alkamar ma.
30 Ku bari su zauna tare har lokacin yanka. A lokacin yanka kuma zan gaya wa masu yankan su fara yanke ciyawar su tara, su ɗaure dami dami a ƙone, alkamar kuwa su taro ta su sa a taskata.’ ”