2 Ga wani ƙaramin littafi a buɗe a hannunsa. Sai ya tsai da ƙafarsa ta dama a kan teku, ƙafarsa ta hagu kuwa a kan ƙasa,
3 ya yi kira da murya mai ƙarfi, kamar zaki yana ruri. Da ya yi kiran, sai aradun nan bakwai suka yi tsawa.
4 Sa'ad da kuwa aradun nan bakwai suka yi tsawa, kamar zan rubuta, sai na ji wata murya daga sama tana cewa, “Rufe abin da aradun nan bakwai suka faɗa, kada ka rubuta.”
5 Sai mala'ikan nan da na gani a tsaye a teku da ƙasa ya ɗaga hannunsa na dama sama,
6 ya rantse da wanda yake a raye har abada abadin, wanda ya halicci sama da abin da take a cikinta, da ƙasa da abin da take a cikinta, da kuma teku da abin da take a cikinta, cewa ba sauran wani jinkiri kuma,
7 sai dai a lokacin busa ƙahon da mala'ika na bakwai zai busa ne, za a cika asirtaccen nufin nan na Allah, bisa ga bisharar da ya yi wa bayinsa annabawa.
8 Sa'an nan muryar nan da na ji daga sama ta sāke yi mini magana, ta ce, “Je ka, ka ɗauki littafin nan da yake a buɗe a hannun mala'ikan da yake a tsaye a bisa teku da ƙasa.”