15 Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”
16 Sai dattawan nan ashirin da huɗu da suke a zaune a kan kursiyansu a gaban Allah suka fādi suka yi wa Allah sujada,
17 Suna cewa,“Mun gode maka, ya Ubangiji Allah, Maɗaukaki,Wanda yake a yanzu, shi ne kuma a dā,Saboda ka ɗauki ikonka mai girma, kana mulki.
18 Al'ummai sun husata, fushinka kuwa ya auko,Lokaci ya yi da za a yi wa matuttu shari'a,A kuma yi wa bayinka, annabawa da tsarkaka sakamako,Da masu jin tsoron sunanka, yaro da babba,A kuma hallaka masu hallaka duniya.”
19 Sa'an nan aka buɗe Haikalin nan na Allah da yake a Sama, aka kuma ga akwatin alkawarinsa a Haikalinsa. Sai aka yi ta walƙiya da kururuwa, da aradu, da rawar ƙasa, da ƙanƙara manya manya.