2 Tana da ciki, sai kuma ta yi ta ƙara ta ƙagauta domin ta haihu, saboda azabar naƙuda.
3 Sai kuma aka ga wata alama a sama, ga wani ƙaton jan maciji mai kawuna bakwai, da ƙahoni goma, da kambi bakwai a kawunansa.
4 Wutsiyarsa ta sharo sulusin taurari, ta zuba su a ƙasa. Sai macijin ya tsaya a gaban matar nan mai naƙuda, don ya lanƙwame ɗan nata in ta haife shi.
5 Ta kuwa haifi ɗa namiji, wanda zai mallaki dukkan al'ummai da sandar ƙarfe, amma aka fyauce ɗan nata, aka kai shi zuwa wurin Allah da kursiyinsa.
6 Matar kuwa, sai ta gudu ta shiga jeji, a inda Allah ya shirya mata wurin da za a cishe ta har kwana dubu da metan da sittin.
7 Sai yaƙi ya tashi a sama, Mika'ilu da mala'ikunsa suna yaƙi da macijin nan, macijin kuma da mala'ikunsa suka yi ta yaƙi,
8 amma aka cinye su, har suka rasa wuri a sama sam.