3 Dukkan al'ummai sun yi tsananin jarabar yin fasikanci da ita,Sarakunan duniya kuma sun yi fasikanci da ita,Attajiran duniya kuma sun arzuta da almubazzarancinta.”
4 Sai na ji wata murya daga Sama, tana cewa,“Ku fito daga cikinta, ya ku jama'ata,Kada zunubanta su shafe ku,Kada bala'inta ya taɓa ku.
5 Domin zunubanta sun yi tsororuwa, sun kai har Sama,Allah kuwa ya tuna da laifofinta.
6 Ku saka mata daidai da yadda ta yi,Ku biya ta ninkin ayyukanta,Ku dama mata biyun abin da ta dama muku.
7 Yadda ta ɗaukaka kanta, ta yi almubazzaranci,Haka ku ma ku saka mata da azaba, da baƙin ciki gwargwadon haka.Tun da yake a birnin zuciyarta ta ce, ‘Ni sarauniya ce, a zaune nake,Ni ba gwauruwa ba ce,Ba ni da baƙin ciki kuma har abada!’
8 Saboda haka, bala'inta zai aukar mata rana ɗaya,Mutuwa, da baƙin ciki, da yunwa.Za a kuma ƙone ta,Domin Ubangiji Allah da yake hukunta ta Mai Ƙarfi ne.”
9 Sarakunan duniya kuma da suka yi fasikanci da zaman almubazzaranci da ita, za su yi mata kuka da kururuwa, in sun ga hayaƙin ƙunarta,