1 Bayan wannan na ji kamar wata sowa mai ƙarfi ta ƙasaitaccen taro a Sama, suna cewa,“Halleluya! Yin ceto, da ɗaukaka, da iko, sun tabbata ga Allahnmu,
2 Don hukuncinsa daidai yake, na adalci ne,Ya hukunta babbar karuwar nan wadda ta ɓata duniya da fasikancinta,Ya kuma ɗauki fansar jinin bayinsa a kanta.”
3 Sai suka sāke yin sowa, suna cewa,“Halleluya! Hayaƙinta yana tashi har abada abadin.”
4 Sai dattawan nan ashirin da huɗu, da rayayyun halittan nan huɗu, suka fāɗi suka yi wa Allah sujada, shi da yake zaune a kan kursiyin, suna cewa, “Amin. Halleluya!”
5 Sai aka ji wata murya daga kursiyin, tana cewa,“Ku yabi Allahnmu, ya ku bayinsa,Ku da kuke jin tsoronsa, yaro da babba.”
6 Sai na ji kamar wata sowar ƙasaitaccen taro, kamar ƙugin ruwa mai gudu, kamar aradu mai ƙara, suna cewa,“Halleluya! Gama Ubangiji AllahnmuMaɗaukaki shi ne yake mulki.