3 ya jefa shi mahallakar, ya rufe, ya kuma yimƙe ta da hatimi, don kada ya ƙara yaudarar al'ummai, har dai shekarun nan dubu su ƙare. Bayan wannan lalle ne a sake shi zuwa ɗan lokaci kaɗan.
4 Sa'an nan na ga kursiyai, da waɗanda aka bai wa ikon hukunci, zaune a kai. Har wa yau, kuma na ga rayukan waɗanda aka fille wa kai saboda shaidar da suka yi wa Yesu, da kuma Maganar Allah, ba su kuwa yi wa dabbar nan da siffarta sujada ba, ba su kuma yarda a yi musu alamarta a goshinsu ko a hannunsu ba, sun sāke rayuwa, sun yi mulki tare da Almasihu har shekara dubu.
5 Sauran matattu kuwa, ba su sāke rayuwa ba, sai bayan da shekaran nan dubu suka cika. Wannan fa shi ne tashin matattu na farko.
6 Duk wanda yake da rabo a tashin nan na farko, mai albarka ne, tsattsarka ne. Mutuwa ta biyu ba ta da iko a kan irin waɗannan, amma za su zama firistocin Allah da na Almasihu, su kuma yi mulki tare da shi har shekara dubu.
7 Bayan shekaran nan dubu sun ƙare, sai a saki Shaiɗan daga ɗaurinsa,
8 ya kuma fito ya yaudari al'ummai waɗanda suke kusurwoyin nan huɗu na duniya, wato, Gog da Magog, ya tattara su saboda yaƙi, yawansu kamar yashin teku.
9 Sai kuma su bazu, su mamaye duk duniya, su yi wa sansanin tsarkaka da ƙaunataccen birni ƙawanya, sai wuta ta zubo daga sama ta lashe su.