1 Sa'an nan Bilatus ya sa a tafi da Yesu, a yi masa bulala.
2 Sai soja suka yi wani kambi na ƙaya suka sa masa a kā, suka yafa masa wata alkyabba mai ruwan jar garura.
3 Suka yi ta zuwa wurinsa, suna cewa, “Ranka ya daɗe, Sarkin Yahudawa!” suna ta marinsa.
4 Sai Bilatus ya sāke fitowa, ya ce wa Yahudawa, “Ga shi, zan fito muku da shi, domin ku san ban same shi da wani laifi ba.”
5 Sa'an nan Yesu ya fito, sāye da kambin ƙayar, da alkyabba mai ruwan jar garura. Sai Bilatus ya ce musu, “To, ga mutumin!”
6 Da manyan firistoci da dogaran Haikali suka gan shi, suka ɗau kururuwa suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce musu, “Ku tafi da shi ku da kanku, ku gicciye shi, ni kam, ban same shi da wani laifi ba.”