10 Yana gama miƙa hadayar ke nan, sai ga Sama'ila ya iso.Saul kuwa ya fita don ya tarye shi, ya gaishe shi.
11 Sai Sama'ila ya ce, “Me ke nan ka yi?”Saul ya amsa ya ce, “Don na ga mutane suna watsewa, suna barina, kai kuma ba ka zo daidai lokacin ba, ga kuma Filistiyawa sun tattaru a Mikmash.
12 Sai na yi tunani cewa, ‘Yanzu Filistiyawa za su gangaro su fāɗa mini a Gilgal, ni kuwa ban riga na roƙi Ubangiji ba,’ don haka ya zama mini tilas in miƙa hadaya ta ƙonawa!”
13 Sama'ila kuwa ya ce wa Saul, “Ka yi wauta, ba ka kiyaye umarnin da Ubangiji Allahnka ya umarce ka da shi ba. Dā Ubangiji ya tabbatar maka da sarautar Isra'ila har abada.
14 Amma yanzu sarautarka ba za ta tabbata ba, gama Ubangiji ya riga ya sami mutum wanda yake so. Ubangiji ya riga ya naɗa shi ya zama sarkin jama'arsa, domin ba ka kiyaye umarnin Ubangiji ba.”
15 Sama'ila ya tashi daga Gilgal zuwa Gibeya ta Biliyaminu. Da Saul ya ƙidaya mutanen da suke tare da shi, ya tarar wajen mutum ɗari shida ne.
16 Sai Saul da ɗansa, Jonatan, da mutanen da suke tare da su suka zauna a Geba ta Biliyaminu. Filistiyawa kuwa suka kafa sansaninsu a Mikmash.