11 Sai ya tambayi Yesse, “Ko kana da sauran waɗansu 'ya'ya maza?”Yesse ya ce, “Da sauran autan, ga shi kuma, yana wurin kiwon tumaki.”Sama'ila ya ce masa, “Sai ka aika a taho da shi, gama ba zan koma ba, sai ya zo.”
12 Yesse kuwa ya aika aka taho da shi. Ga shi kuwa kyakkyawa ne, idanunsa suna sheƙi. Sai Ubangiji ya ce wa Sama'ila, “Tashi ka zuba masa man keɓewa, shi ne sarkin.”
13 Sama'ila ya ɗauki man zaitun, ya zuba masa a gaban 'yan'uwansa. Ruhun Ubangiji ya sauko da iko a kan Dawuda tun daga wannan rana zuwa gaba. Sama'ila kuwa ya tashi, ya koma Rama.
14 Yanzu kuwa Ruhun Ubangiji ya rabu da Saul, sai Ubangiji ya sa mugun ruhu ya azabtar da shi.
15 Barorin Saul kuwa suka ce masa, “To, ga shi yanzu, Ubangiji ya sa mugun ruhu na azabtar da kai.
16 Saboda haka muna so ka ba mu izini mu tafi, mu nemo mutum gwanin kiɗan garaya, domin sa'ad da mugun ruhun nan da Allah ya sa maka, ya hau kanka, sai ya kaɗa maka garayar don ya sauka.”
17 Saul kuwa ya ce wa barorinsa. “To, sai ku samo mini mutum gwanin kiɗa, ku kawo mini shi.”