21 Ubangiji ya sa wa Hannatu albarka, ta haifi 'ya'ya maza uku da mata biyu. Yaron nan Sama'ila kuwa ya girma a gaban Ubangiji.
22 Eli kuwa ya tsufa ƙwarai, yana kuma jin dukan abin da 'ya'yansa maza suke yi wa Isra'ilawa, da yadda suke kwana da matan da suke aiki a ƙofar alfarwa ta sujada.
23 Sai ya ce musu, “Me ya sa kuke irin waɗannan abubuwa? Gama kowa yana faɗa mini irin mugayen abubuwan da kuke aikatawa.
24 Haba 'ya'yana, ku bari! Jama'ar Ubangiji suna ta magana a kan wannan mugun abu.
25 Idan mutum ya yi wa wani laifi, Allah yakan kāre shi, amma idan mutum ya yi wa Ubangiji zunubi, wa zai kāre shi?”Amma ba su ji maganar mahaifinsu ba, gama Ubangiji ya riga ya yi shirin kashe su.
26 Yaron nan Sama'ila ya yi ta girma da samun tagomashi a gaban Ubangiji da kuma mutane.
27 Wani annabi ya zo wurin Eli da saƙo daga wurin Ubangiji ya ce, “Sa'ad da kakanka Haruna da iyalinsa suke bauta wa Fir'auna a Masar, na bayyana kaina gare shi.