13 Amma idan har mahaifina yana da niyyar yi maka mugunta, amma ban sanar da kai ba, to, bari Ubangiji ya hukunta ni. Ubangiji ya kasance tare da kai kamar yadda ya kasance da mahaifina.
14 Ba lokacin da nake da rai ne kaɗai za ka nuna mini alherin Ubangiji domin kada in mutu ba.
15 Ko bayan raina kada ka daina nuna wa gidana alheri har abada, lokacin da Ubangiji ya datse maƙiyanka daga fuskar duniya.”
16 Jonatan ya yi alkawari da gidan Dawuda. Ubangiji kuwa zai ɗauki fansa a kan maƙiyan Dawuda.
17 Sai Jonatan ya sa Dawuda ya yi masa alkawari zai ƙaunace shi, gama shi kansa yana ƙaunar Dawuda ƙwarai kamar yadda yake ƙaunar kansa.
18 Sa'an nan Jonatan ya ce wa Dawuda, “Gobe ce amaryar wata, ba kowa a wurin zamanka ke nan da yake ba za ka zo ba.
19 A rana ta uku za a gane ba ka nan sosai, to, sai ka tafi, ka ɓuya a wurin da ka ɓuya a waccan rana. Ka zauna kusa da tarin duwatsu.