4 Dawuda kuma ya sāke roƙon Ubangiji. Sai Ubangiji ya amsa masa, ya ce, “Tashi, ka gangara zuwa Kaila, gama zan ba da Filistiyawa a hannunka.”
5 Sa'an nan Dawuda da mutanensa suka tafi Kaila, suka yi yaƙi da Filistiyawa, suka kashe su da yawa, suka kwashe shanunsu. Da haka Dawuda ya kuɓutar da mazaunan Kaila.
6 Lokacin da Abiyata ɗan Ahimelek, ya gudu zuwa wurin Dawuda a Kaila, ya zo da falmaran a hannunsa.
7 Aka faɗa wa Saul Dawuda ya zo Kaila. Sai ya ce, “Madalla, Allah ya bashe shi a hannuna, gama ya kulle kansa, da yake ya shiga garin da yake da ƙofofin da akan kulle da sandunan ƙarfe.”
8 Saul ya kirawo dukan mutanensa, su fita yaƙi, su tafi Kaila don su kewaye Dawuda tare da mutanensa.
9 Dawuda kuwa ya sani Saul yana shirya hanyar kashe shi, sai ya ce wa Abiyata, firist, “Kawo falmaran a nan.”
10 Sa'an nan ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, hakika bawanka ya ji Saul yana niyyar zuwa Kaila don ya hallakar da garin saboda ni.