14 Shin, sawun wa Sarkin Isra'ila yake bi? Wane ne kuma kake runtuma? Kana bin sawun mataccen kare, da sawun tunkuyau?
15 Ubangiji ne zai zama alƙali, ya hukunta tsakanina da kai. Zai tsaya mini, ya cece ni daga hannunka.”
16 Da Dawuda ya gama faɗa wa Saul wannan magana, sai Saul ya ce, “Ɗana, Dawuda, muryarka ke nan?” Ya yi kuka da ƙarfi.
17 Sa'an nan ya ce wa Dawuda, “Ka fi ni adalci, gama ka yi mini alheri, ni kuwa na yi maka mugunta.
18 Yau ka nuna a sarari yadda ka yi mini alheri. Ubangiji ya bashe ni a hannunka, amma ba ka kashe ni ba.
19 Idan mutum ya sami maƙiyinsa, zai bar shi ya tafi lafiya? Ubangiji ya sāka maka saboda alherin da ka yi mini yau.
20 Yanzu kuwa na sani za ka zama sarki, sarautar Isra'ila za ta kahu a hannunka.