18 Yau ka nuna a sarari yadda ka yi mini alheri. Ubangiji ya bashe ni a hannunka, amma ba ka kashe ni ba.
19 Idan mutum ya sami maƙiyinsa, zai bar shi ya tafi lafiya? Ubangiji ya sāka maka saboda alherin da ka yi mini yau.
20 Yanzu kuwa na sani za ka zama sarki, sarautar Isra'ila za ta kahu a hannunka.
21 Sai ka rantse mini da Ubangiji, cewa ba za ka hallaka zuriyata a bayana ba, ba kuwa za ka shafe sunana daga cikin gidan ubana ba.”
22 Dawuda kuwa ya yi wa Saul alkawari.Sa'an nan Saul ya koma gida, amma Dawuda da mutanensa suka koma wurin ɓuya.