1 Sama'ila kuwa ya rasu. Dukan Isra'ilawa suka taru suka yi makoki dominsa. Suka binne shi a gidansa a Rama.Sai Dawuda ya tashi ya tafi jejin Faran.
2 Akwai wani mutumin Mawon wanda yake da harka a Karmel. Mutumin mai dukiya ne ƙwarai, yana da tumaki dubu uku (3,000) da awaki dubu (1,000). Yana yi wa tumakinsa sausaya a Karmel.
3 Sunan mutumin kuwa Nabal, sunan matarsa kuma Abigail, ita haziƙa ce, kyakkyawa, amma mijinta miskili ne, marar mutunci. Shi daga zuriyar Kalibu ne.
4 Daga cikin jeji, Dawuda ya ji, wai Nabal yana yi wa tumakinsa sausaya,
5 sai ya aiki samari goma, ya ce musu, “Ku tafi Karmel wurin Nabal, ku ce ina gaishe shi.
6 Gaisuwar da za ku yi masa ke nan, ku ce, ‘Salama gare ka, salama ga gidanka, salama kuma ga dukan abin da kake da shi.