15 Ga shi, mutanen kuwa sun yi mana kirki, ba mu sha wata wahala ba, ba abin da ya ɓace mana dukan lokacin da muke tare da su a jeji.
16 Sun zama mana ganuwa dare da rana dukan lokacin da muke tare da su a wurin kiwon tumaki.
17 Yanzu sai ki yi tunani, ki san abin da ya kamata ki yi, gama ana niyyar yi wa maigida da dukan gidansa ɓarna. Ga shi, maigida yana da mugun hali, ba zai ji kowa ba!”
18 Sai Abigail ta yi sauri, ta ɗauki malmalar abinci guda metan, da salkar ruwan inabi biyu, da tumaki biyar da aka gyara, da soyayyen hatsi mudu uku, da nonnan 'ya'yan inabi guda ɗari, da kauɗar ɓaure guda metan, ta labta wa jakai.
19 Ta ce wa samarin, “Ku yi gaba, ga ni nan tafe bayanku.” Amma ba ta faɗa wa Nabal, mijinta ba.
20 Tana tafiya a kan jaki, ta kai gindin wani dutse ke nan, sai ga Dawuda da mutanensa tafe. Ta tafi, ta sadu da su.
21 Dawuda ya ce a ransa, “Ashe, a banza ne na yi ta lura da dukan abin da yake na mutumin nan a jeji, har ba abin da yake nasa da ya ɓace. Ga shi, ya rama mini alheri da mugunta.