21 Sa'an nan Saul ya ce, “Na yi laifi, ka komo, ɗana Dawuda, ba zan yi maka kome ba, gama raina ya zama da daraja a gare ka kyau. Na yi aikin wauta, na yi laifi da yawa.”
22 Sai Dawuda ya ce, “Ga mashinka! Ka aiko wani saurayi ya zo ya karɓa.
23 Ubangiji dai zai sāka wa kowa bisa ga adalcinsa da amincinsa. Ubangiji ya bashe ka a hannuna yau, amma na ƙi in kashe wanda Ubangiji ya keɓe.
24 Kamar yadda ranka ya zama da daraja a gare ni yau, bari raina kuma ya zama da daraja a gaban Ubangiji, ya cece ni daga dukan wahala.”
25 Sai Saul ya ce wa Dawuda, “Ubangiji ya sa maka albarka, ɗana Dawuda, za ka yi manyan abubuwa, ka kuwa yi nasara!”Dawuda dai ya yi tafiyarsa, Saul kuma ya koma gidansa.