1 Sa'ad da Dawuda da mutanensa suka koma Ziklag a rana ta uku, sai suka tarar Amalekawa sun riga sun kawo wa Negeb da Ziklag hari. Suka cinye Ziklag, suka ƙone ta.
2 Suka kwashe mata da dukan waɗanda suke ciki manya da ƙanana, suka tafi da su. Ba su kashe kowa ba, amma suka kwashe su, suka tafi.
3 Da Dawuda da mutanensa suka ga an ƙone garin, an kuma kwashe matansu, da 'ya'yansu mata da maza ganima,
4 sai suka yi ta kuka da ƙarfi, har ƙarfinsu ya ƙare.
5 An kwashe matan Dawuda biyu ganima, wato Ahinowam Bayezreyeliya da Abigail Bakarmeliya, matar Nabal wanda ya mutu.