11 Mutanen Dawuda suka sami wani Bamasare a karkara, suka kawo shi wurin Dawuda. Suka ba shi abinci da ruwa, ya ci ya sha.
12 Suka kuma ba shi kauɗar ɓaure da nonnan inabi biyu. Da ya ci sai ya wartsake, gama ya yi yini uku da dare uku ba ci ba sha.
13 Dawuda kuwa ya tambaye shi, “Wane ne ubangidanka? Daga ina ka fito?”Ya amsa, ya ce, “Ni saurayi ne, Bamasare, baran wani Ba'amaleke. Kwana uku ke nan da ubangidana ya tafi ya bar ni a baya saboda ba ni da lafiya.
14 Mun kai hari a Negeb ta Keretiyawa ta Yahuza, da Negeb ta Kalibu, muka kuma ƙone Ziklag.”
15 Dawuda ya ce masa, “Za ka yarda ka kai ni wurin maharan nan?”Sai ya ce wa Dawuda, “Idan ka rantse mini da Allah, ba za ka kashe ni ba, ba kuwa za ka mai da ni wurin ubangidana ba, sai in kai ka inda maharan nan suke.”
16 Ya kai Dawuda a wurinsu, sai ga su nan a baje ko'ina a ƙasar, suna ci, suna sha, suna rawa, saboda ganima mai yawa da suka kwashe daga ƙasar Filistiyawa da ƙasar Yahuza.
17 Sai Dawuda ya yi ta karkashe su tun faɗuwar rana har zuwa kashegari da yamma. Ba wanda ya tsira daga cikinsu sai samari ɗari huɗu waɗanda suka tsere a kan raƙuma.