1 Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra'ilawa. Isra'ilawa kuma suka yi gudun Filistiyawa, aka karkashe su a Dutsen Gilbowa.
2 Filistiyawa suka ci Saul da 'ya'yansa maza. Suka kashe Jonatan, da Abinadab, da Malkishuwa, 'ya'yan Saul.
3 Yaƙin ya matsa wa Saul. Maharba suka harbe shi, suka yi masa mummunan rauni.
4 Sai ya ce wa mai ɗaukar masa makamai, “Ka zare takobinka ka sha zarata da shi domin kada marasa kaciyan nan su zo su sha zarata, su yi mini ba'a.” Amma mai ɗaukar masa makamai bai yarda ba, domin ya ji tsoro da yawa. Sai Saul ya zare takobinsa, ya faɗa a kansa.
5 Da mai ɗaukar masa makamai ya ga Saul ya rasu, shi ma ya fāɗa a kan nasa takobi ya mutu tare da Saul.
6 Haka Saul, da 'ya'yansa maza guda uku, da mai ɗaukar masa makamai, da dukan mutanen da suke tare da shi suka mutu a rana ɗaya.