11 Aka kuma ƙwace akwatin alkawarin Ubangiji, 'ya'yan Eli guda biyu, Hofni da Finehas kuma, aka kashe su.
12 Wani mutumin kabilar Biliyaminu ya gudu daga dāgar yaƙin ya zo Shilo da tufafinsa ketattu ga kuma ƙura a kansa.
13 Sa'ad da ya iso, Eli yana zaune a kujerarsa a bakin hanya, yana jira, gama zuciyarsa ta damu saboda akwatin alkawarin Allah. Da mutumin ya shiga gari ya ba da labari, dukan garin ya ruɗe da kuka.
14 Sa'ad da Eli ya ji kukan, sai ya tambaya ya ce, “Me ake wa kuka?” Mutumin kuwa ya gaggauta zuwa wurin Eli ya faɗa masa.
15 (Eli yana da shekara tasa'in da takwas, ya kuwa makance ɗungum.)
16 Mutumin ya ce wa Eli, “Yau daga wurin yaƙin na tsere, na gudo gida.”Eli ya ce, “Dana, me ya faru?”
17 Sai wanda ya kawo labarin ya ce, “Isra'ilawa sun gudu a gaban Filistiyawa, an kashe mutane da yawa, har ma da 'ya'yanka biyu, Hofni da Finehas, sun rasu, an kuma ƙwace akwatin alkawarin Allah.”