5 Da akwatin alkawarin Ubangiji ya iso sansanin, sai dukan mutanen Isra'ila suka yi sowa da ƙarfi, har ƙasa ta amsa.
6 Da Filistiyawa suka ji amon sowar suka ce, “Ina ma'anar irin wannan babbar sowa a sansanin Ibraniyawa?” Da suka gane akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga sansanin,
7 sai Filistiyawa suka tsorata, suka ce, “Allah ya shiga sansanin, kaitonmu, gama ba a taɓa yin irin wannan abu ba.
8 Mun shiga uku, wa zai cece mu daga hannun allolin nan masu iko? Waɗannan suka karkashe Masarawa a hamada!
9 Ya ku Filistiyawa, ku yi ƙarfin hali, ku yi jaruntaka don kada ku zama bayin Ibraniyawa kamar yadda suka zama bayinku, ku yi jaruntaka ku yi yaƙi.”
10 Filistiyawa kuwa suka yi yaƙi gadan-gadan, suka ci mutanen Isra'ila. Mutanen Isra'ila suka gudu, kowa ya nufi gidansa. Aka kashe Isra'ilawa da yawa, wato mutum dubu talatin (30,000).
11 Aka kuma ƙwace akwatin alkawarin Ubangiji, 'ya'yan Eli guda biyu, Hofni da Finehas kuma, aka kashe su.