1 Da Sama'ila ya tsufa, sai ya naɗa 'ya'yansa maza su zama alƙalan Isra'ila.
2 Sunan ɗansa na fari Yowel, na biyun kuma Abaija. Su ne alƙalai a cikin Biyer-sheba.
3 Amma 'ya'yansa ba su bi gurbin mahaifinsu ba, amma suka mai da hankalinsu ga neman kuɗi, suka yi ta cin hanci, suka danne gaskiya.
4 Dukan shugabannin Isra'ila kuwa suka tattaru, suka tafi wurin Sama'ila a Rama,
5 suka ce masa, “Ga shi, ka tsufa, ga kuma 'ya'yanka ba su bi gurbinka ba, yanzu dai sai ka naɗa mana sarki wanda zai yi mulkinmu kamar sauran ƙasashe.”
6 Amma Sama'ila bai ji daɗin roƙonsu ba, na a naɗa musu sarki, saboda haka ya yi addu'a ga Ubangiji.
7 Ubangiji kuwa ya ce masa, “Sai ka kasa kunne ga dukan abin da suka faɗa maka, gama ba kai suka ƙi ba, amma ni suka ƙi da zama sarkinsu.