6 Amma Sama'ila bai ji daɗin roƙonsu ba, na a naɗa musu sarki, saboda haka ya yi addu'a ga Ubangiji.
7 Ubangiji kuwa ya ce masa, “Sai ka kasa kunne ga dukan abin da suka faɗa maka, gama ba kai suka ƙi ba, amma ni suka ƙi da zama sarkinsu.
8 Irin abubuwan da suke yi maka, irinsu ne suka yi mini tun daga ranar da na fito da su daga Masar har wa yau, sun ƙi ni, suka yi ta bauta wa gumaka.
9 Yanzu dai sai ka saurari maganarsu kurum, amma ka faɗakar da su sosai da sosai, ka kuma nuna musu irin halin sarkin da zai sarauce su.”
10 Sama'ila kuwa ya faɗa wa mutanen da suke roƙo ya naɗa musu sarki dukan abin da Ubangiji ya faɗa.
11 Ya ce musu, “Ga irin halin sarkin da zai sarauce ku, zai sa 'ya'yanku maza su zama sojojinsa, waɗansunsu za su yi aiki da karusan yaƙinsa, waɗansu su zama mahayan dawakansa, da masu kai hari musamman.
12 Waɗansu kuma zai sa su zama shugabannin mutum dubu dubu da na hamsin hamsin. 'Ya'yanku ne za su riƙa yi masa noma da girbi, su ƙera masa kayayyakin yaƙi da na karusansa.