12 Amma saboda tsohonka, Dawuda, ba zan ƙwace a zamaninka ba, amma zan ƙwace daga hannun ɗanka.
13 Duk da haka ba zan ƙwace mulkin duka ba, amma zan ba ɗanka kabila guda, saboda bawana Dawuda, saboda kuma Urushalima wadda na zaɓa.”
14 Ubangiji kuwa ya sa Hadad Ba'edome, ya tayar wa Sulemanu. Shi Hadad daga jinin sarautar Edom ne.
15 Gama sa'ad da Dawuda ya ci Edom, Yowab, shugaban sojoji, ya tafi don ya binne kisassu, sun yi wata shida a can, shi da mutanensa, sai ya kashe kowane namijin da yake cikin Edom.
16 Gama Yowab da dukan Isra'ilawa sun tsaya a Edom wata shida, sai da ya gama kashe mazajen Edom duka.
17 Amma Hadad ya tsere zuwa Masar tare da waɗansu Edomawa, barorin tsohonsa. Hadad yana ɗan saurayi a lokacin.
18 Suka kama hanya daga Madayana suka zo Faran. Daga Faran suka kwashi mutane tare da su, suka tafi Masar zuwa wurin Fir'auna, Sarkin Masar, wanda ya ba shi gida, ya kuma riƙa ba shi abinci, ya kuma ba shi ƙasa.