18 Suka kama hanya daga Madayana suka zo Faran. Daga Faran suka kwashi mutane tare da su, suka tafi Masar zuwa wurin Fir'auna, Sarkin Masar, wanda ya ba shi gida, ya kuma riƙa ba shi abinci, ya kuma ba shi ƙasa.
19 Hadad kuwa ya sami farin jini ƙwarai a wurin Fir'auna, har ya aurar masa da ƙanwar matarsa, wato ƙanwar Tafenes, sarauniya.
20 Ita kuwa ta haifa masa ɗa, Genubat, wanda Tafenes ta yi renonsa a gidan Fir'auna. Genubat kuwa ya zauna tare da 'ya'yan Fir'auna, maza.
21 Amma sa'ad da Hadad ya ji labari Dawuda ya rasu, Yowab shugaban sojoji shi ma ya rasu, sai Hadad ya ce wa Fir'auna, “Ka yardar mini, in tashi, in koma ƙasata.”
22 Amma Fir'auna ya ce masa, “Me ka rasa a nan har da kake so ka koma ƙasarka?”Hadad ya ce masa, “Ka dai yardar mini kawai in tafi.” Ya kuwa koma ƙasarsa.
23 Allah kuma ya sa Rezon ɗan Eliyada, ya tayar wa Sulemanu, shi Rezon ya gudu daga wurin maigidansa, Hadadezer Sarkin Zoba.
24 Ya tattara wa kansa mutane ya zama shugaban 'yan hari bayan kashe-kashen da Dawuda ya yi. Sai suka tafi Dimashƙu, suka zauna a can, suka naɗa shi Sarkin Dimashƙu.