20 Sauran ayyukan Zimri da makircin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
21 Jama'ar Isra'ila suka rabu biyu. Rabi suka bi Tibni ɗan Ginat don su naɗa shi sarki. Rabin kuwa suka bi Omri.
22 Amma jama'ar da suka bi Omri suka rinjayi waɗanda suka bi Tibni ɗan Ginat. Sai Tibni ya mutu, Omri kuwa ya zama sarki.
23 A shekara ta talatin da ɗaya ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Omri ya ci sarautar Isra'ila. Ya yi shekara goma sha biyu yana sarauta. Ya yi shekara shida yana mulki a Tirza.
24 Sa'an nan ya sayi tudun Samariya daga Shemer a bakin azurfa dubu shida (6,000), a wurin Shemer, ya kuwa yi gini a kan tudun, ya sa masa suna Samariya saboda sunan Shemer mai tudun.
25 Omri kuwa ya aikata mugunta a gaban Ubangiji fiye da dukan waɗanda suka riga shi.
26 Ya bi duk irin hanyoyin Yerobowam ɗan Nebat, da irin zunuban da ya sa jama'ar Isra'ila su yi. Suka sa Ubangiji Allah na Isra'ila ya yi fushi saboda gumakansu.