23 Huram kuma ya yi kewayayyiyar babbar kwatarniya ta zubi da tagulla. Faɗinta kamu goma ne, tsayinta kuwa kamu biyar, da'irarta kuma kamu talatin ne.
24 Akwai goruna kewaye da gefensa. Gora goma a kowane kamu ɗaya. Suka kewaye kwatarniya. Gorunan jeri biyu ne, an yi zubinsu haɗe da kwatarniyar.
25 Aka ɗora ta a kan siffofin bijimai goma sha biyu. Siffofin bijimai uku suna fuskantar gabas, uku kuma suna fuskantar yamma, uku suna fuskantar kudu, uku kuma suna fuskantar arewa. An ɗora kwatarniya a kansu. Gindinsu duka na wajen ciki.
26 Kaurin kwatarniya ya kai taƙin hannu guda. An yi gefenta kamar finjali, kamar kuma furen bi-rana. Takan ci garwa dubu biyu.
27 Ya kuma yi dakali goma da tagulla. Kowane dakali tsawonsa kamu huɗu, faɗinsa kuma kamu huɗu, tsayinsa kuwa kamu uku ne.
28 Yadda aka yi dakalan ke nan, dakalan suna da sassa, sassan kuma suna da mahaɗai.
29 Aka zana hotunan zakoki, da na bijimai, da na kerubobi a kan sassan. A kan mahaɗan kuma akwai gammo, aka zana hotunan furanni a ƙarƙashin zakokin da bijiman.