7 Ya kuma gina shirayi ta sarauta inda zai riƙa yin shari'a, ya rufe dukan daɓenta da itacen al'ul.
8 Ya gina gidan da zai zauna a farfajiya na ciki, wajen shirayi. ya kuma gina wa matarsa, 'yar Fir'auna, gida irin wannan.
9 Aikin gine-ginen nan, an yi shi da duwatsu masu tamani tun daga tushen har zuwa rufin. Sai da aka auna duwatsun sa'an nan aka yanka su da zarto, ciki da baya daidai da juna.
10 An kafa harsashin ginin da manyan duwatsu masu tsada, waɗansu kamu takwas waɗansu goma.
11 Daga sama kuma akwai duwatsu masu tsada waɗanda aka yanka su bisa ga ma'auni, da kuma itacen al'ul.
12 Babbar farfajiyar fāda, da filin Haikali na ciki da shirayin Haikalin yana da bangaye da jerin katakan al'ul domin kowane jeri uku na yankakkun duwatsu.
13 Sarki Sulemanu kuwa ya aika a kawo Huram daga Taya, gwanin aikin tagulla ne.