28 Duk da haka, ya Ubangiji Allahna, ka ji addu'ata, ni bawanka, da roƙe-roƙena, ka ji kukana da addu'ata da nake yi a gabanka yau.
29 Domin ka riƙa duban Haikalin nan dare da rana, wurin da ka ce sunanka zai kasance domin ka riƙa jin addu'ar da bawanka zai yi yana fuskantar wurin.
30 Sai ka riƙa jin roƙe-roƙen bawanka da na mutanenka Isra'ilawa, idan sun yi addu'a, suna fuskantar wurin nan, sa'ad da ka ji kuma, sai ka gafarta musu.
31 “Idan mutum ya yi wa maƙwabcinsa laifi, aka ba shi rantsuwa, idan ya zo, ya rantse a gaban bagadenka a wannan Haikali,
32 ya Ubangiji ka ji daga Sama, ka shara'anta bayinka, ka hukunta mai laifin, ka ɗora masa hakkinsa a kansa, amma ka kuɓutar da mara laifin, ka sāka masa bisa ga adalcinsa.
33 “Lokacin da abokan gāba suka ci mutanenka Isra'ila da yaƙi, saboda sun yi maka zunubi, idan sun komo wurinka, suka yabe ka, suka yi addu'a, suka roƙe ka a wannan Haikali,
34 sai ka ji daga Sama, ka gafarta wa jama'ar Isra'ila zunubinsu, sa'an nan ka sāke komar da su zuwa ƙasar da ka ba kakanninsu.