48 Idan sun komo gare ka da zuciya ɗaya, da dukan ransu a ƙasar abokan gabansu waɗanda suka kai su bauta, suka yi addu'a gare ka, suna fuskantar ƙasarsu wadda ka ba kakanninsu, da birnin da ka zaɓa, da Haikalin da na gina saboda sunanka,
49 sai ka ji addu'arsu da roƙe-roƙensu daga Sama, wurin zamanka, ka amsa, ka ji ƙansu.
50 Ka gafarta dukan zunubansu, da tayarwar da suka yi maka. Ka sa abokan gabansu su ji tausayinsu.
51 Gama su jama'arka ne, mallakarka, waɗanda ka fito da su daga Masar, daga tsakiyar azaba.
52 “Ya Ubangiji Allah, ka dubi jama'arka Isra'ila da sarkinsu da idon rahama, ka kasa kunne gare su duk lokacin da suka yi roƙo a gare ka.
53 Gama ka keɓe su daga sauran dukan al'ummai domin su zama jama'arka kamar yadda ka faɗa ta bakin bawanka Musa, sa'ad da ka fito da kakanninmu daga Masar.”
54 Da Sulemanu ya gama wannan addu'a da roƙo ga Ubangiji, sai ya tashi daga gaban bagaden Ubangiji, inda yake a durƙushe da hannuwansa a miƙe zuwa sama.