12 Dawuda kuma ya ce wa Uriya, “Ka kwana nan kuma yau, gobe in sallame ka.” Sai Uriya ya kwana a Urushalima a ran nan.
13 Kashegari kuma Dawuda ya kira shi liyafa. Ya zo, ya ci ya sha tare da shi, har Dawuda ya sa shi ya bugu. Amma da dare, sai ya tafi ya kwanta a shimfiɗarsa tare da sauran barorin sarki, amma bai tafi gidansa ba.
14 Da safe Dawuda ya rubuta wasiƙa, ya ba Uriya ya kai wa Yowab.
15 A wasiƙar ya ce wa Yowab, “Tura Uriya a gaba a inda yaƙin ya fi zafi, sa'an nan ku ja da baya, ku bar shi don a buge shi a kashe shi.”
16 Sa'ad da Yowab yake kama garin da yaƙi, sai ya sa Uriya a inda ya sani akwai jarumawan gaske.
17 Mutanen garin suka fito suka yi yaƙi da Yowab. Suka kashe waɗansu daga cikin sojojin Dawuda. Uriya Bahitte, shi ma aka kashe shi.
18 Sai Yowab ya aika aka faɗa wa Dawuda labarin yaƙin.