15 Saboda mutane sun tsorata ni shi ya sa na zo in faɗa wa ubanjijina, sarki. Na kuwa yi tunani na ce, ‘Zan tafi in faɗa wa sarki, watakila sarki zai amsa roƙona.
16 Gama sarki zai ji, ya cece ni daga hannun mutumin nan da zai hallaka ni tare da ɗana daga cikin jama'ar Allah.’
17 Na kuma yi tunani a kan maganar ubangijina, sarki, za ta kwantar da zuciyata, gama ubangijina, sarki, kamar mala'ikan Allah yake, yana rarrabe tsakanin nagarta da mugunta. Ubangiji Allahnka ya kasance tare da kai!”
18 Sai sarki ya ce mata, “Kada ki rufe mini duk abin da zan tambaye ki.”Ta ce, “To, ka yi tambayarka.”
19 Sa'an nan ya ce mata, “Ko akwai hannun Yowab cikin dukan sha'anin nan naki?”Ita kuwa ta amsa, “Na rantse da kai, ya ubangijina, sarki, ba dama a yi maka ƙumbiya-ƙumbiya. Haka ne, Yowab baranka ne ya sa ni. Shi ya sa dukan waɗannan magana a bakin baranyarka.
20 Yowab baranka ya yi wannan don ya daidaita al'amarin. Amma ubangijina yana da hikima irin ta mala'ikan Allah domin ya san dukan al'amuran da suke a duniya.”
21 Sa'an nan sarki ya ce wa Yowab, “To, na yarda, sai ka tafi ka komo da saurayin nan, Absalom.”