16 Sa'an nan Yowab ya busa ƙaho, sojoji suka komo daga runtumar Isra'ilawa. Yowab ya tsai da su.
17 Suka ɗauki gawar Absalom, suka jefa ta cikin wani rami mai zurfi a kurmin, suka tula tsibin duwatsu a kanta. Dukan Isra'ilawa kowa ya tsere zuwa gidansa.
18 Tun Absalom yana da rai ya gina wa kansa al'amudi a kwarin sarki, gama ya ce, “Ba ni da ɗa wanda zai sa a riƙa tunawa da ni.” Ya kira al'amudin da sunansa. Ana kuwa kiransa al'amudin Absalom har wa yau.
19 Ahimawaz ɗan Zadok ya ce wa Yowab, “Ka yarda mini in sheƙa a guje in kai wa sarki labari yadda Ubangiji ya cece shi daga hannun magabtansa.”
20 Yowab ya ce masa, “Ba za ka kai labari yau ba, sai wata rana ka kai, amma yau ba za ka kai labari ba, domin ɗan sarki ya mutu.”
21 Sa'an nan Yowab ya ce wa wani mutumin Habasha, “Tafi ka faɗa wa sarki abin da ka gani.” Sai Bahabashen ya rusuna wa Yowab, sa'an nan ya sheƙa a guje.
22 Ahimawaz ɗan Zadok kuma ya ce wa Yowab, “Ko mene ne zai faru dai, ka bar ni in bi bayan Bahabashen a guje.”Yowab ya ce masa, “Don me za ka tafi, ɗana, tun da yake ba za ka sami lada saboda labarin da za ka kai ba?”