28 Da Ahimawaz ya zo kusa da sarki, ya ce, “Salama!” Sa'an nan ya rusuna a gaban sarki ya sunkuyar da fuska ƙasa, ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka, wanda ya ba da mutanen da suka tayar wa ubangijina, sarki.”
29 Sai sarki ya ce, “Na ce dai, saurayin nan, Absalom, yana nan lafiya?”Ahimawaz ya amsa, ya ce, “A sa'ad da Yowab ya aiko ni na ga babban hargitsi, amma ban san ko mene ne ba.”
30 Sarki kuwa ya ce, “Koma waje ɗaya, ka tsaya.” Sai ya koma waje ɗaya ya tsaya cik.
31 Sai ga Bahabashe ya iso, ya ce, “Abishirinka, ya ubangijina, sarki, gama a wannan rana ta yau Ubangiji ya cece ka daga hannun waɗanda suka tayar maka.”
32 Sarki ya tambaye shi, “Na ce dai, saurayin nan Absalom, yana lafiya?”Bahabashen ya amsa, “Allah ya sa abokan gāban ubangijina, sarki, da duk waɗanda suka tayar maka da mugunta, su zama kamar saurayin nan.”
33 Sai zuciyar sarki ta tsinke, ya hau cikin ɗakin da yake kan garun ƙofar garin yana ta kuka, yana cewa, “Ya ɗana Absalom, ɗana! Wayyo, ɗana Absalom! Da ma ni ne na mutu, ba kai ba. Ya Absalom, ɗana, ɗana!”