35 A yau ina da shekara tamanin cif. Ba zan iya in rarrabe abu mai daɗi da marar daɗi ba. Ba kuma zan iya ɗanɗana daɗin abin da nake ci ko abin da nake sha ba. Ba zan iya jin daɗin muryar mawaƙa ba. Zan zamar maka kaya kurum, ranka ya daɗe.
36 Ban cancanci wannan irin babban lada ba. Zan dai yi maka 'yar rakiya zuwa hayin Urdun.
37 Ina roƙonka ka bar ni in koma domin in rasu a garinmu, kusa da kabarin mahaifina. Amma ga Kimham barana, bari ya tafi tare da kai, ranka ya daɗe. Ka yi masa yadda kake so.”
38 Sarki ya ce, “To, Kimham zai tafi tare da ni, zan kuwa yi masa abin da zai yi maka daɗi. Duk abin da kake so a gare ni, zan yi maka.”
39 Sa'an nan dukan jama'a suka haye Urdun, sarki kuma ya haye. Ya yi bankwana da Barzillai, ya sumbace shi, ya kuma sa masa albarka. Sai Barzillai ya koma gidansa.
40 Sarki kuwa ya yi tafiya zuwa Gilgal. Kimham kuma ya tafi tare da shi. Mutanen Yahuza duka, da rabin mutanen Isra'ila suna tafe tare da sarki.
41 Sai dukan mutanen Isra'ila suka zo wurin sarki, suka ce masa, “Me ya sa mutanen Yahuza 'yan'uwanmu, suka sace ka, suka kawo sarki da iyalinsa a wannan hayin Urdun, tare da dukan mutanensa?”